Tuwon semonvita da alabo da miyar kubewa danya

Mrs Ghalee Tk Cuisine
Mrs Ghalee Tk Cuisine @cook_13808718
Jos
Tura

Kayan aiki

  1. Garin semonvita Kofi biyu
  2. Garin alabo Kofi biyu
  3. Kayan hadin miyar
  4. Manja Rabin kofi
  5. Kubewa
  6. Pomo
  7. Daddawa guda uku
  8. Cardamom guda uku
  9. White pepper guda Sha biyu
  10. Citta guda biyu yan daidai
  11. Albasa yan daidai guda biyu
  12. Attatuhu guda uku
  13. Duddubin Nama(irin kasan Naman layyan nan)
  14. Tokan sanyi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko ki zuba ruwa a tukunya ki rufe ya tafasa idan ya tafasa kiyi talge ki zuba

  2. 2

    Ga talgen na na dama Zan zuba

  3. 3

    Sai ki gauraya ki rufe ki barshi ya nuna Amma ba ruf ba saboda ze iya zubewa

  4. 4

    Gashi nan ya nuna Sai ki zuba alabo ki tuka

  5. 5

    Gashi nan na tuka Sai na rufe na rage wuta tsawon minti 15 zuwa 20

  6. 6

    Gashi nan yayi Zan sake tukawa

  7. 7

    Sai ki bude leda ki deban tuwon ki xuba ki kulle

  8. 8

    Ga kayan da nai amfani dasu

  9. 9

    Dafarko ki Nika su citta da daddawa da white pp da cardamom. Sannan kiyi blending albasa da attatuhun ki ki ajiye a gefe

  10. 10

    Ki zuba manja a tukunya idan yayi zafi ki zuba jajjagen albasa da attatuhun ki soya

  11. 11

    Sannan ki zuba duddubin Naman ki gauraya

  12. 12

    Ki zuba garin su daddawan da Kika Nika ki soya na tsawon minti 5

  13. 13

    Sai ki zuba ruwa ki rufe ya tafasa

  14. 14

    Sai ki dauko pomo ki zuba sannan kisa magi

  15. 15

    Sannan ki wanke kubewa ki goga a abun gogawa,Kamar haka

  16. 16

    Sai ki zuba a ruwan miyanki da yake ta tafasa sannan kisa maburgi ki burge

  17. 17

    Ki rufe Amma ba ruf ki barshi kubewan ta nuna

  18. 18

    Saura minti biyar ki sauke Sai ki zuba tokan sanyi ki kadan(amfani tokan sanyi Yana da yawa zesa miyan yayi yauki sosai sannan yafi kanwa amfani ajiki),ki gauraya Sai ki rufe Amma ba ruf ba

  19. 19

    Miyar ki tayi

  20. 20

    Aci dadi lafiya

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Mrs Ghalee Tk Cuisine
Mrs Ghalee Tk Cuisine @cook_13808718
rannar
Jos

Similar Recipes