Dambun couscous

Hauwa Kasim
Hauwa Kasim @Houwwerh

Girkin gargajiya

Tura

Kayan aiki

35minuts
7-8 yawan abinchi
  1. Couscous Leda biyu
  2. gwangwaniMai rabin
  3. 8Maggi
  4. Curry chokali 1½
  5. Gishiri
  6. Zogale
  7. Albasa
  8. Attaruhu
  9. Tafarnuwa
  10. Gyada
  11. Ruwa
  12. Salak,tumatir,albasa, cucumber

Umarnin dafa abinci

35minuts
  1. 1

    Zaki zuba couscous dinki acikin container, se ki zuba Mai acikinsa kijuuashi sosai seki ajiyeshi agefe

  2. 2

    Sannan ki gyara zogalenki,kiyanka albasa,ki jajjaga attaruhu duk ki ajiyesu agefe

  3. 3

    Sannan ki dauko couscous din da muka zubawa Mai Adan yayyafa masa ruwa basosaiba yayi danshi

  4. 4

    Sannan ki dauko maggi,gishiri,curry,gyada dakakkiya ki zuba aciki ki juyasu sosai ya juyu,ki kara yayyafa wani ruwan akai

  5. 5

    Bayan kinyi haka se kidauko attaruhunki kizuba aciki kijuya tare da albasa,zogale ko cabbage kijuyasu sosai komai yazama yayi daidai

  6. 6

    Sannan kikara yayyafa masa wani ruwan akai yyi danshi sosai amman kar ruwan yyi yasa sbd kar ya chabe mana
    Bayan kingama se kidauko abin da kikegin dambun dashi ko madanbaci ki zuba wannan hadin damukayi aciki ki rufesa kar kibar hanyar da tururi ze fito daga ciki Sanna ki Dora akan wuta
    Kar wutar tayi yawa sosai kuma kartayi kadan

  7. 7

    Bayan yyi kamar mintuna 20 akai seki bude kingani ki kara yayyafa masa wani ruwan kadan ki juyashi yajuyu sannan ki kara rufewa daganan baze wuce 10-15 minutes ba zaki saukeshi tunda shi bashida wahalar dahuwa

  8. 8

    Bayan kingama se kiyi hadin salad dinki kizuba agefe
    Idan kinaso ana iya hadawa da wake agefe yana dadi sosai amman shi optional ne

  9. 9

    Note: idan amfanin zuba Mai afarko yana hanashi chabewa zeyi wara wara kamar dambun shinkafa sannan ruwan kadan kadan ake zubawa sbd kar yyi yawa

  10. 10

    Nagode sosai taku akullum
    Hauwa kassim👩‍🍳

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hauwa Kasim
Hauwa Kasim @Houwwerh
rannar

sharhai (4)

Similar Recipes