Onion Rings - Zoben Albasa

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Sokoto State

Albasa na cikin lokacin ta gara muyi amfani da ita kafin ta fara tsada 😉 gashi kuma ina son cin wani abu me gishiri gishiri ba zaki zaki ba #albasa #onion #onionrings #zobenalbasa

Onion Rings - Zoben Albasa

Albasa na cikin lokacin ta gara muyi amfani da ita kafin ta fara tsada 😉 gashi kuma ina son cin wani abu me gishiri gishiri ba zaki zaki ba #albasa #onion #onionrings #zobenalbasa

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

Minti 30mintuna
2 yawan abinchi
  1. Flour cup 1
  2. 1Tandori spoon
  3. 2Albasa manya
  4. 3Maggi
  5. 1Ajino moto spoon
  6. Mai na suya
  7. Ruwa kadan kadan
  8. Corn four chokai 1 (ba dole ba ne)
  9. Yaji gari

Umarnin dafa abinci

Minti 30mintuna
  1. 1

    Kisamu albasa manya guda 2ki yanke sama da qasa

  2. 2

    Ki daka maggi kala 3 yayi gari sosai

  3. 3

    Ki hada cikin flour da kika tankade ki yanka albasa sala sala

  4. 4

    Se ki hada duka ki sa ruwa kadan kadan

  5. 5

    Ki dama da fork kada yayi kolullai

  6. 6

    Yayi laushi sosai

  7. 7

    Albasan shima zaki raba shi daya bayan daya

  8. 8

    Se ki jefa albasa cikin kwabin ki

  9. 9

    Ki lullube ta duka

  10. 10

    Sanna ki jefa daya bayan daya cikin mai kada kisa da yawa don ze sha mai

  11. 11

    Ki soya duka gefen kina juyawa se ki kwashe

  12. 12

    Ki saka a rayiya ya tsane mai

  13. 13

    Ki bar shi bis plate kafin wani ya soyu se ki barbada yaji ki ci

  14. 14

    Zaki iya barbada ma albasar flour kafin ki jefa cikin kullun flour kada tasha mai

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Jamila Ibrahim Tunau
rannar
Sokoto State
The kitchen is my comfort zone.
Kara karantawa

Similar Recipes