Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa kofi biyu
  2. Wake kofi daya
  3. Kwai guda uku
  4. Ajino daya
  5. Gishiri cokali daya
  6. Lattas
  7. Tumatir
  8. Albasa
  9. Cucumber
  10. Yajin barkwano
  11. Mangyada
  12. 1/4Ruwan kanwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ga abubuwan danayi amfani dasu nan

  2. 2

    Da farko na gyara wake na zuba a ruwan dumi sai na dora akan wuta

  3. 3

    Yayi kamar minti 30 sannan nasa ruwan kanwa

  4. 4

    Bayan minti sha biyar sai na sauke na tsiyaye ruwan

  5. 5

    Ga shi nan zan dora ruwan shinkafa amma sai na kulle kwai a leda nasa a ciki na dora akan wuta

  6. 6

    Da ruwan ya tafasa sai na zuba shinkafa na gauraya na rufe

  7. 7

    Bayan wasu mintuna sai na zuba dafaffen waken nan na gauraya na rufe

  8. 8

    Nabashi minti goma sai na juye a matsami

  9. 9

    Na zuba ruwa a tukunya nazuba gishiri da ajino na rufe har saida ya tafasa sannan na zuba shinkafa da waken gauraya su gu daya

  10. 10

    Bayan wasu mintuna garau garau dina ya dahu

  11. 11

    Na yanka lattas tumatir cucumber albasa da kwai dafaffe

  12. 12

    Ga hadin salad dressing nasa maggie star daya dakakken masaro rabin cokalin shan shayi da bama cikin cokalin cin abinci da man gyada shima cikin cokalin cin abinci biyu

  13. 13

    Gashi nan na hadasu gu guaya na gauraya

  14. 14

    Ga shinan na zuba hadin akan salad din

  15. 15

    Zgashi nan na gauraya

  16. 16

    Gashi nan na gama komai na zuba komai a mazubin sa

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mrs Ghalee Tk Cuisine
Mrs Ghalee Tk Cuisine @cook_13808718
rannar
Jos

Similar Recipes