Bredin fulawa

Ummu_Zara
Ummu_Zara @ummu_zaraskitchen
Sokoto State

#Bakedbread Yarana nason biredi matuka shiyasa nake yimusu

Bredin fulawa

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

#Bakedbread Yarana nason biredi matuka shiyasa nake yimusu

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 2Fulawa cofi
  2. Sugar babban cokali 2
  3. Yeast babban cokali 1
  4. cokaliMai babban

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Ki auna fulawa cofi 2 ki tankade

  2. 2

    Ki auna sugar da yeast ki hada guri daya, kisa ruwan dumi ki garwayasu, kibarshi ya tashi na minti 5

  3. 3

    Ki fasa Kwai kisa cikin tankadaddar fulawar, ki sa Mai, kisa hadin yeast da sugar

  4. 4

    Sai ki mulkashi kinayi kina sa ruwa kadan kadan kina mulkawa har sai hade da ya bar Kama hannu, sai ki rufe ki ajiye a wurin dumi kibarshi ya tashi na minti 20, zakiga girmanshi ya karu

  5. 5

    Ki shafa Mai ga abin gashi Dan kada ya kama, sai ki mulmula yadda kikeso ki aza kan pan, ki gasa a oven

  6. 6

    Za'a iya ci da Miya ko tea, ko wani abin sha

  7. 7

    Ga cikinshi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu_Zara
Ummu_Zara @ummu_zaraskitchen
rannar
Sokoto State
sunana Rukayya Ashir saniIna son yin girki kala-kala, Abubuwa da yawa dangane da kitchen suna burgeni.
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes