🥗Dambun Shinkafa🥗

Maryam Abdullahi
Maryam Abdullahi @maryammamu
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Shinkafa barjajjiya kofi 2
  2. Zogala
  3. Tarugu 5
  4. tattasai 3
  5. Albasa 1
  6. Tafarnuwa
  7. Kayan kamshi
  8. Mai
  9. Maggie
  10. Maggi ajino
  11. Curry
  12. Thyme
  13. Gishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki Kai Shinkafa a6arzata anikata dai dai yadda kike so. Idan annikata saiki saka rariya ki tankade shinkafan zaki ga gari na fita sai ki zubarda garin kiyi aiki da shinkafan.

  2. 2

    Sai ki wanke shinkafan ki tsaneta akwando, sai ki wanke zogala ki zuba aciki ki yanka albasa sai ki motsa,

  3. 3

    Kisami madambaci ki shinfida Leda kamin ki saka shi sai ki zubashi aciki ki aza ruwa atukunya saiki aza madambacin ciki

  4. 4

    Sai ki rufe da marfi kiduba da kyau idan akwai wajenda Bai rufuba sai ki kwana kuka ki rufe wanjen.

  5. 5

    Ki jajjaga tattasai tarugu albasa da tafarnuwa iya yawan yadda kikeso sai ki yanka albasa.

  6. 6

    Kibarshi ya dahu harsai zogalan ya Fara dahuwa sai ki sauke ki zuba a roba.

  7. 7

    Sai ki zuba Mai ki motsa Amman bada yawa BA yadda dai Zai Nuna kinsa Mai.

  8. 8

    Sai ki sauke. Shikenan dambun shikafa ya kammala🥘🥗😋

  9. 9

    Sai ki hada maginki dasu curry da kayan kamshi ki dakasu saiki zuba su cikin dambun ki motsa sosai saiki dauko tarugunki da kika jajjaga ki zuba ciki.

  10. 10

    Sai ki motsasu sosai harsu hade jikinsu sosai

  11. 11

    Sai ki sake mayar dashi a madambacin ki mayar awuta ki barshi ya dahu sosai idan ya dahu zakiji yafara kamshi

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Maryam Abdullahi
Maryam Abdullahi @maryammamu
rannar

Similar Recipes