Cooking Instructions
- 1
Wanan itace masarar da akeyin gugguru da ita, ba irin masarar yin tuwo bace, ita wanan ja ce kuma bata kai farar masara girma ba, zaki wanke ki zubar da ruwan sanan ki jika ta tsawon minti biyar.
- 2
Sai ki bazata ta bushe sosai.
- 3
Zaki dora tukunya akan wuta, ki zuba butter, flavor da siga idan yai zafi sai ki zuba masarar ki rage wutar,zaki rufe da murfi kina tsaye akan tukunyar zakiji ta fara fashewa(popping) tana tsalle sai ki ringa jijjiga tukunyar a hankali, idan kika ji shiru to alamar ta gama fashewa sai ki bude tukunyar ki juye.Zaki barbade da madarar gari ki ci.
- 4
Ga yanda masarar zatayi idan an samu matsaloli kamar haka:Idan wuta tayi yawa sai masarar ta kone ba tare da sun fashe ba, idan masarar bata bushe ba kika zuba a tukunya to bazata fashe ba illa ta kone, idan tukunyar da kikayi amfani karama ce dan haka idan masarar ta fara fashewa zata ci ka, kuma ragowar da basu fashe ba suna qasa sai su kone.
Similar Recipes
-
-
-
California Farm Tiger Shrimp with Peas in Ginger California Farm Tiger Shrimp with Peas in Ginger
Quick seared large frozen tiger shrimp in ginger butter with tender young frozen peas and lemon juice, a ten minute tasty fresh summer farm dinner. Hobby Horseman -
-
-
Caramel crunch pop corn Caramel crunch pop corn
Easy way to make microwave popcorn in minutes! I'm adding peanuts next time! :chef Calypso Spirit
More Recipes
Comments