Farfesun kifin hausa

mum afee's kitchen
mum afee's kitchen @cook_17411383

Inason Farfesun kifin Hausa sosai Saboda zaka iya cinsa da ko wani irin abinci😋

Farfesun kifin hausa

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan

Inason Farfesun kifin Hausa sosai Saboda zaka iya cinsa da ko wani irin abinci😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

20mintuna
Kifi
  1. Kifi tarwada
  2. Sinadarin dandano
  3. Gishiri
  4. Citta
  5. Kanufari
  6. Tafarnuwa
  7. Farin mai
  8. Albasa
  9. Attaruhu
  10. Tattasai

Umarnin dafa abinci

20mintuna
  1. 1

    Da farko zan fara wanke kifina da ruwa Mai dan zafi zan zuba masa Saboda yafi Saurin fita,daganan nasa masa gishiri na kara wankewa da ruwa Mai kyau har sai ya fita saina tsane Shi a kwando Dan ya tsane

  2. 2

    Saina dauko kayan miyana na jajjaga su sosai sai na kara Yanka albasa a kwanno Mai kyau, na dauko citta da kanufari na daka su sosai

  3. 3

    Saina dauko Wannan kifin na dan sa masa gishiri da citta da kanufari na juyasa sosai sai na rufe sa Saboda karni na saka masa kayan hadin da na fada

  4. 4

    Bayan na jajjaga kayan miya na, sai na dura tukunya a wuta na zuba Mai saina juye kayan miyan nan a ciki na suya su sosai saina zuba Ruwa yadda nake so

  5. 5

    Saina rufe tukunyar Danya tafasa, idan ya tafasa saina sa Sinadarin dandano da gishiri kadan da citta,kanufari,tafarnuwa a ciki saina rufe dan Yan kara dahuwa

  6. 6

    Saina dauko kifin na zuba acikin tukunyarnan na dauko albasarnan dana yanka na wake na zuba aciki na juya sosai ma dan barsa Ya dahu kadan

  7. 7

    Idan ya dahu a sauke shikenan sai ci

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
mum afee's kitchen
mum afee's kitchen @cook_17411383
rannar

sharhai

Similar Recipes