Awara

 Dada Hafsat( Hana's Ktchn )
Dada Hafsat( Hana's Ktchn ) @cook_19590080
Kaduna

# Team tree awara Nada muhimmanci ga jikin Dan Adam sosai musamman inta samu kayan lambu

Awara

# Team tree awara Nada muhimmanci ga jikin Dan Adam sosai musamman inta samu kayan lambu

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

awa biyua
5 zuwa 6 yadang
  1. 4Waken suya Kofi
  2. Yaji
  3. Ruwan tsami na tatan koko
  4. 5Tarugu
  5. 5Tattasai
  6. Tumatir
  7. 3Albasa matsakaita guda
  8. 2Maggi
  9. chokali Gishiri Rabin karamin
  10. 1Onga karamin cokali
  11. Mai Rabin kwalba
  12. 4Manja cokali
  13. Kabeji
  14. Latas

Umarnin dafa abinci

awa biyua
  1. 1

    Zaa tsince wake a cire dauda sannan a jika da ruwan dumi minti 30

  2. 2

    Sannan akaishi a markado idan an dawo asa manja a chakuda sannan a zuba cikin gyallen tata a tace

  3. 3

    Sannan a zuba a tukunya adora kan wuta a rufe abarshi yaci gaba da dahuwa

  4. 4

    Bayan an Dora kan wuta yafara alaman tafasa sannan a wanke kayan miya a jajjaga a zuba ciki a batshi yaci gaba da huwa harya tafaso sai a zuba ruwan tsamin zaaita zubawa har awara ta hade inta dahu zaaga alaman ba fari Yakoma kaman kalan ruwan tsamin

  5. 5

    Idan ta hade jikinta sai a kwashe cikin gyallen tata a kulle saman a barshe ta tsame da kanta sannan a yanka akuma jika maggi gishiri da onga adinga tsomata ciki

  6. 6

    Zaa Dora mai a wuta idan yayi zafi adinga sakawa ciki ana soyawa idan gefe yayi sai a juya dayan gefen inyayi sai a tsameshi a matsami abatshi mai ya tsane

  7. 7

    Agefe guda kuma zaa yanka cabeji da albasa kadan da tumatir sai kuma a yanka latas gefe guda shi kadai a zuba awara a faranti a sa kayan hadi a gefe yaji a gefe sai latas a saman awara

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
 Dada Hafsat( Hana's Ktchn )
rannar
Kaduna
I love cooking morethan any thing else, caterers we feed the world
Kara karantawa

Similar Recipes