Nan bread da ferfeaun kafan shanu

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Yana daya daga cikin abincin da maigida yafiso sosai shiyasa ina yawan yimasa shi

Tura

Kayan aiki

  1. Fulawa kofi uku
  2. Butter
  3. Kwai daya
  4. chokaliYeast babban
  5. chokaliTumeric rabin
  6. Habbatus sauda
  7. Madarar gari chokali uku
  8. Baking powder dan kadan
  9. Gishiri dan kadan
  10. Sugar chokali daya da rabi
  11. Milk flavor
  12. Vanillah flavor
  13. Ruwa kofi daya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki samo bowl sai kizuba ruwan aciki sannan kisa sugar da yeast kikada sannan kizuba milk flavor

  2. 2

    Sai kisake kadawa sannan kisa vanillah flavor da kwai sai ki jujjuya kirufe ki ajiye agefe

  3. 3

    Sannan kitankade fulawa kizuba a babban bowl ko roba sai kizuba madara kurkur gishiri da baking powder sannan ki jujjuyashi komai yahade a wuri daya

  4. 4

    Sannan sai kidauko ruwan yeast din zakiga tatashi takumbura sai kidan juyashi sannan kizuba akan fulawar sai ki kwabashi sosai sannan kidauko butter kizuba akai kici gaba da kwabawa har tayi laushi sosai

  5. 5

    Bayan kingama kwabawa sai kirufe ki ajiye agefe na sawon awa daya sannan kidauko zakiga yatashi sosai sannan kisake kwabawa sai kiringa yankan kadan kadan kina mulmulawa sannan ki murzata tayi flat kamar haka sannan kiwatsa habba akai kisake murzawa sai kisaka a pan kina gasawa idan dayan gefen yayi sai kijuya dayan shima yagasu

  6. 6

    Haka zakiyi tayi har kigama kuma zaki iya cinta haka kokuma da duk kalar miyar da kikeso.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

sharhai (3)

Maman jaafar(khairan)
Maman jaafar(khairan) @jaafar
To inajira 😋😋
🤣🤣🤣🤣haka zakice kena

Similar Recipes