Sinasir da hadin miyan Irish carrot and cabbage

Mrs Mubarak
Mrs Mubarak @maanees_kitchen

#teamsokoto nayi wannan girkin ne saboda yarah sun matsa maanee ayi muna mai kamr masa irin nna masan kwai 😅😅😅

Sinasir da hadin miyan Irish carrot and cabbage

#teamsokoto nayi wannan girkin ne saboda yarah sun matsa maanee ayi muna mai kamr masa irin nna masan kwai 😅😅😅

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Farar shinkafa
  2. Kwai
  3. Baking powder
  4. Yeast
  5. Flour
  6. Cabbage
  7. Sinadarin dandano
  8. Nama
  9. Mai
  10. Tattasai
  11. Tarugu
  12. Albasa
  13. Carrot
  14. Irish
  15. Gishiri

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Na jiqa farar shinkafa ta tsawon wasu awowi bayan na tabbatar da yayi yanda nake bukata na wanke

  2. 2

    Na dauko dafaffen shinkafa da zanyi dauri dashi na hade su wuri daya

  3. 3

    Na zuba yeast da flour na hadesu duka wuri daya na markada saida yy laushi, na barshi na minti biyar ya kara tashi

  4. 4

    Bayannan na daura kaskon tuya a wuta yayi zafi na fara zuba kullun aciki,sannan na rufe na wasu dakiku na bude na juiya dayan gefen

  5. 5

    Haka nayi tayi har kullun ya kare

  6. 6

    Na tafasa nama na na yanka Irish kananu na kuma yanka carrot da cabbage

  7. 7

    Na jajjaga kayan miyan na yanka albasa

  8. 8

    Na zuba mai a wuta na kawo jajjage na zuba nadan soya sama sama nayi sanwa nasaka kayan dandano da kanshi

  9. 9

    Sannan na zuba tafassashen nama da kuma Irish da carrot na barshi tawon 10mint

  10. 10

    Bayan nan na bude naga ya fara nuna sai na zuba yankakken cabbage da albasa na motsa 2mint sai na sauke

  11. 11

    Shikenan miyan ya kammala

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mrs Mubarak
Mrs Mubarak @maanees_kitchen
rannar

sharhai (5)

Similar Recipes