Kayan aiki

  1. Waken suya gwangwani 4
  2. 1/8 cupManja
  3. Kanwa kadan
  4. 1/2 tspDan tsami

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki gyara wake sai ki wanke shi sosai ki rage sai kisa kanwa kadan ki markada.

  2. 2

    Idan aka markada miki sai ki zuba manja aciki ki kara ruwa sai kisa mataci ki tace sosai sai ki juye madara acikin tukunya ki daura akan wuta, sai ki jiga dan tsami da ruwa da zarar ya tafasa sai ki dakko dan tsami ki zuba aciki ba'a juyawa da kanta zata hade sai ki barta akan wuta zakiga tana hadewa a hankali a hankali idan ta gama yi zakiga ruwan ya koma garai garai sai ki dakko mataci ki juye aciki sai ki daure bakin mataci ki ajjiye a gefe zakiga ruwan yanata tsanewa a hankali shikkenan.

  3. 3

    Gashi bayan tayi ruwan ya kuma garai garai sai a tace a maci.

  4. 4

    Shikkenan kin gama awara sai ki yankata kisa a ruwan maggi da gishiri sai ki soya ko kisa a fridge.

  5. 5

    Gashi nan bayan na soya sai aci da iyali.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Aysher Babangida (Ayshert Cuisines)
rannar
Kano

Similar Recipes