Jallof rice&vegetables &lemon zobo

Taufiqa Said
Taufiqa Said @cook_35293874
Tura

Kayan aiki

hr 1 da mint 30mintuna
3 yawan abinchi
  1. 2Shinkafa kofi
  2. Tsokar nama
  3. Vegetables
  4. Kabeji
  5. Kayan dandano
  6. Kayan miya markadadde
  7. Ganyen zobo
  8. Watermelon
  9. Cucumber
  10. Sugar &flavor
  11. Abinci

Umarnin dafa abinci

hr 1 da mint 30mintuna
  1. 1

    Da farko nama na fara yankawa kanana sai na Dora shi a wuta na xuba albasa isasshiya da maggi da curry da spice na rufe na barshi ya dahu

  2. 2

    Na Dora wata tukunyar na xuba ruwa bayan ya tafasa na xuba shikafa tayi rabin dahuwa sai na tace ta a colander

  3. 3

    Sai kuma na maida tukunyar na xuba mai da kayan miya na soya su sannan na xuba naman da na dafa da ruwansa sannan na xuba wannan shinkafar na xuba vegetables din da na yanka da kuma albasa wadda na yanka slice sannan na juya sosai na dauko tafasasshen ruwa na xuba ya dan hau kan shinkafar sannan na rage wutar sosai na rufe har komai ya yi laushi.

  4. 4

    Shi kuma lemo na dafa ganyen zobo na zuba fresh Ginger da kaninfari a cikin dahuwarsa sannan na bare kankana na zuba a blender na yanki cucumber kamar kwata na hada na markada su sosai sai da suka yi laushi na juye ba tare da na tace ba na juye ruwan zobo akai na saka a fridge bayan ya yi sanyi na zuba sugar da flavor shi kenan na gama hadadden zobo mai dadin gaske

  5. 5

    Sai na yanka kabeji na kankare bayan karas na gurza shi sai cucumber kanana na zuba cream salad da bama

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Taufiqa Said
Taufiqa Said @cook_35293874
rannar

sharhai (2)

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Ga bayani dalla dalla mun gode 😋 barka da shan ruwa 🌙

Similar Recipes