Tura

Kayan aiki

2 awa
5 yawan abinchi
  1. Kan saniya an gyara an wanke
  2. Attaruhu 5
  3. tattasai 3
  4. albasa 2
  5. Maggi
  6. gishiri
  7. citta
  8. tafarnuwa
  9. da sauran kayan kamshi
  10. Ruwa yanda zai dafa shi yayi luguf

Umarnin dafa abinci

2 awa
  1. 1

    Da farko ki wanke gyararren kan saniyarki ki dora a wuta da ruwa kadan in ya tafasa ki zubar da ruwan

  2. 2

    Sai ki mayar dashi wuta ki zuba kayan hadinki duka na barshi yayi ta dahuwa har sai da naga ruwan ya ja sosa naman kumai yayi laushi

  3. 3

    Sai na sauke.in ruwan ya janye be dahu ba zaki iya kara masa ruwa yadda zai dafa shi.aci dadi lapia

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hafsatmudi
Hafsatmudi @Hafsatmah08
rannar
Bauchi

sharhai (2)

Similar Recipes