Farfesun naman kan rago

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Kan rago
  2. Attaruhu
  3. Albasa
  4. Manja
  5. Gyada mai gishiri
  6. Daddawa
  7. Maggi
  8. Gishiri
  9. Suga
  10. Kayan kamshi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Da farko zaki wanke naman kai tatas da soson karfe sabo duk baki-bakin nan ya fita saiki zuba a tukunya yayita dahuwa har sai yayi laushi saiki kwashe ki zuba a kwando.

  2. 2

    Saiki daura wata tukunyar ki zuba manja ki yanka albasa ki zuba, saiki gyara attaruhun ki ki wanke ki jajjaga zuwa man janki ya soyu saiki cire albasar ki zuba attaruhun ki saka ludayi ki jujjuya ki rage wutar, saiki samu wannan dafaffen naman kai din ki kara wanke shi saiki juye cikin tukunyar ki saiki zuba ruwa dai-dai wanda zai isheki ki yanka albasa ki wanke ki zuba ki saka kayan kamshi saiki daka daddawa ma ki zuba, suyita dahuwa.

  3. 3

    In naman ya dauko yi saiki saka maggi da gishiri da d'an suga kadan ba yadda zai bata dandano ba saiki murmushe gyada mai gishiri, ki daka ta tayi laushi ki zuba cikin farfesun ki rage wutar yayita dawuta harya karasa shikenan kin gama zaki iyaci da biredi ko gurasa.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Umma Sisinmama
Umma Sisinmama @cook_14224461
rannar
Kano
I was born in kano state
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes