Tuwon semo  miyar kuka

chef_jere
chef_jere @cook_14164764
Kaduna

Tuwo dai abincin mu ne hausawa Kuma yana da dadi balle ma ace miyar ta kuka ce ba a magana sai an cinye

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

  1. Garin semo yadda zata isheki
  2. Mai gyada
  3. Mai ja
  4. Daddawa chokali daya babba
  5. Garin chitta chokali daya karami
  6. Tafarnuwaguda uku
  7. Tarugu guda biyar
  8. 3tattassai guda
  9. Albasa guda daya
  10. 5Maggi kala Kala guda
  11. Ruwa da zai isheki anfani tuwo da miya
  12. Garin kuka
  13. gwangwaniWake rabin
  14. Nama

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Farko dai zaki daura tukunyar tuwonki a wuta ki zuba ruwa ki diga mai gyada sai ki rufe ya tafasa saiki dauko garin semo ki zuba kina juyawa(ba talge zakiyi ba tazarce zakiyi Kita zuba garin har sai yayi miki kaurin da kikeson tuwonki)sai ki rufe ya dan salala sannan ki zo ki kwashe ki kulla a leda kisa a kuka.

  2. 2

    Saiki dawo ma miyar ki,ki daura tukunya a wuta saiki zuba mai ja da daddawa da garin citta in ya soyu sai ki zuba jajjagen tarugu da albasa da tattasai da tafarnuwa ki jujjuya sai ki zuba ruwa da yawa kaman kofi uku ko hudu,sai ki dauko waken ki ki daddakata kar tayi laushi saiki zuba,sai ki wanke nama ki zuba sai kisa maggi guda uku(zamuyi amfani da guda biyar ne amma uku zaki fara sakawa)saiki rufe tukunyar

  3. 3

    Idan ya tafasa Sosai ruwan ya kone sai ki Kara ruwa kadan ki zuba sauran maggin ki saiki Kara rufe tukunyar in ya tafasa kadan saiki dauko kukar ki saiki amfani da maburgi ki kada miyarki sai ta dan salala kaman na minti 3 saiki sauke ki zuba a plate kici da jus me sanyi ko ruwa

  4. 4

    In an gama ci ayi brush hahaha😂😂😂😂

Yanayi

Gyara girkin
See report
Tura

sharhai

Wanda aka rubuta daga

chef_jere
chef_jere @cook_14164764
rannar
Kaduna
Cooking nd baking are my passion 💪
Kara karantawa

Similar Recipes

More Recommended Recipes