Alkubus mai kayan miya

Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜
Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜 @fatumar6855
Zaria City, I'm Married💞💞💞

Abin marmari ne, shiyasa kowa sai da ya Dana, suna santi😋😋😋😋

Alkubus mai kayan miya

Masu dafa abinci 100+ sun ziyarci wannan girkin

Abin marmari ne, shiyasa kowa sai da ya Dana, suna santi😋😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

5 yawan abinchi
  1. 4 cupsFlour
  2. 1 tspYeast
  3. Salt kadan
  4. Alayyahu
  5. Kayan miya
  6. Maggi
  7. Mai kayan kamshi
  8. Manja
  9. Daddawa
  10. Diyar miya

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki nika kayan miyanki ki soya manja idan ya,soyu ki zuba kayan miyan kisa barking powder saboda ya kashe tsami, ki soya.

  2. 2

    Sai ki tsaida ruwan sanwa, amma kadan saboda ba,aso tayi ruwa sosai, sai ki sa maggi da kayan kamshi, ki daka daddawa da diyar miya ki rufe, sai ki wanke kifinki ki zuba,ki rufe ya tausa.

  3. 3

    Ki yanka alayyahu da albasa, ki wankeshi sosai ki tsane, idan komai ya dahu sai ki cire kifin don kar ya ruguje ki zuba alayyahu ki juya,kisa kifi da curry ki barshi for 2 minutes ki sauke.

  4. 4

    Sai ki zuba flour a roba, kisa yeast da gishiri a gefe,Karki hada su lokaci daya,sai ki samu ruwan dumi, ki rika zubawa kadan kina kwabawa kar yayi ruwa, tafi kwabin fankaso kauri kadan, sai kisa a rana don ya taso.

  5. 5

    Sai ki jajjaga tarugu da albasa ki aje, idan kk ga ya taso,sai kidauko ki zuba jajjagen ki, ki juyashi sosai.

  6. 6

    Sai ki samu gwangwani na cake k shafe shi da mai ki rika zubawa a ciki.

  7. 7

    Sai ki daura tukunya ki zuba ruwa a kasa ki samu basket ki daura a sama, sai ki jera gwangwani kamar zakiyi alale, ki rufe da leda da murfi, ki barshi for 10-15 minutes,ki dauki ashana ki tsira zakiga babu komai alamun ya dahu sai ki sauke. Ki ciccire.

  8. 8

    Enjoy💃💃💃💃💃😋😋😋😋

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Ummu HIBBAAN🍝🍓🍉🍇🍌🍜
rannar
Zaria City, I'm Married💞💞💞
kullum inason koyan abin da ban iya ba, kuma ina son gwadawa🍕🍤🍗🍜🍡🍝
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes