Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. waken suya
  2. Alum/dan tsami / ruwan tsami
  3. Albasar
  4. Attaruhu
  5. Tafarnuwa
  6. Yaji
  7. Mai
  8. Kwai (in kina so)
  9. Mataci / abun tata

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Farko xaki gyara waken ki ki wanke ki markada a bulanda dinki in me kwari ce don kar ya lalata miki idan kuma babu ki bayar a kai miki markade kawae bayan an kawo ki dan diga manja kadan a ciki ki dakko tukunyar da xakiyi a ciki ki saka matacin ki da kika wanke ki juye markaden ki ta ce sosae ki dauraye ki dora a wuta

  2. 2

    Dama kin riga da kin jika alum dinki ko dan tsamin ki in kuma da ruwan tsami xakiyi wato ruwan gasara seki aje duk abinda kike da shi a gefe yana tafasowa ki tsaya akanta don karta xube seki bude ki xuba abinda xakiyi da shi gwargwadon yadda xe isheki ki maida ki rufe ki dan barta ta dan kara dahuwa in kika bude xakiga ta hade seki dakko attaruhu albasar da kuma tafarnuwa da kika riga kika gyara kika wanke kika jajjaga ki xuba

  3. 3

    Se ki dakko matacin ki ki kara juyeta a ciki ki daure ki samu dutse ki dora mata ko dae abu me nauyi akai ko kuma ki samu busa ki sakaleta a jiki ki barta kamar awa daya in kuma kina sauri rabin awa amma fa ki tabbatar dae tsane seki yanka yadda kike so ki fasa kwai ki dinga sakawa a ciki kina soyawa amai ko kuma ki soya haka base kin saka kwan ba shikkenan sekici da yaji da su albasar da tumatur

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Smart Culinary
Smart Culinary @Smartculinary2000
rannar
Johor Bahru Malaysia
Kasan ce da mu a koda yaushe dan samun kyatattun girke girke masu armashi cikin Harshen hausa Tsantsa mun gode 🥰🥰
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes