Farfesun kan rago

Mai dafa abinci 1 yana shirin yin wannan
Mufeeda
Mufeeda @cook_17361783
Kaduna

#NAMANSALLAH
Naman Kai da kafan rago na daga cikin Naman layya, wanda mutane da dama basa bashi mahimmanci, da yawa kyautar da shi suke, wasu Kuma basa ci kwata kwata, ni Kuma nakan yi farfesun shi bayan an kwana biyu da sallah saboda a ganina babu girmamawa da za a wa naman Kai Wanda ya wuce ayi farfesu kasancewar ina matukar son farfesun Naman Kai, a takaice ma, shine farfesun da na fi so sama da kowane irin farfesu, musanman idan na sameshi a kalaci, nakan hada shi da burodi ko waina ko sinasir ko Kuma na ci shi hakanan

Kara karantawa
Gyara girkin
See report
Tura

Kayan aiki

awa 1mintuna
4 yawan abinchi
  1. Naman kai da kafan rago
  2. Tarugu
  3. Albasa
  4. Tafarnuwa
  5. Gishiri
  6. Sinadarin dandano (knorr)
  7. Bay leaf
  8. Pepper soup spice
  9. Scent leaves

Umarnin dafa abinci

awa 1mintuna
  1. 1

    Za a wanke naman sosai har sai ya fita tas (a tabbatar a cire fatan saman halshe, da Kuma kofato).

  2. 2

    Sai a wanke scent leaves a yanka su a ajiye a gefe. Sai a jajjaga ko a markada tarugu, da albasa, da tafarnuwa.

  3. 3

    Sai a daura wannan wankakken naman a kan wuta, a juye jajjagen kayan miyan a ciki, sai a sa gishiri dai dai gwargwado, sai a zuba sinadarin dandano.

  4. 4

    Bayan haka sai a zuba ruwa gwargwadon yanda ze isa dafa naman. Sai a rufe tukunyan, a barshi ya dahu kaman misalin minti 40.

  5. 5

    A yayin da ya fara dahuwa, bayan wadannan mintuna, sai a zuba pepper soup spice, sannan sai a sa bay leaves a ciki, a sake rufewa, a barshi ya dahu kimanin mintuna 10 ko har sai yayi laushi.

  6. 6

    Idan ya dahu, za a lura da wasu naman sun fara sakin jikin kashin, sai a zuba wannan scent leaves din da a ka yanka aka wanke. Sai a barshi ya Kara mintuna 5 yanda dahuwa. Sai a sauke, ana iya ci da burodi ko waina ko sinasir ko Kuma hakanan.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan

sharhai

Wanda aka rubuta daga

Mufeeda
Mufeeda @cook_17361783
rannar
Kaduna

Similar Recipes

More Recommended Recipes