Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

mutun 5 yawan abinchi
  1. Makaroni
  2. Man gyada
  3. Maggi
  4. Gishiri da curry
  5. Alayyaho
  6. Attarugu da tattasai
  7. Albasa se
  8. Ruwa

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki daka / Nika kayan miyanki seki daura tukunya awuta

  2. 2

    Ki zuba man gyada da Dan albasa bayan ya soyu sekisa kayan miyan Suma ki soya sannan seki zuba ruwa Dede Wanda kikasan ze dafa Miki

  3. 3

    Bayan ruwa ya tafasa seki zuba Maggi gishiri curry da Kuma makaronin ki seki juya bayan minti kaman daya ko sakan 30 seki Kara juyawa saboda karya kwanta akasan tukunya

  4. 4

    Bayan ya dahu sekisa Yan kakken alayyahunki ki Dan motsa seki rufe ya salala seki sauke.

  5. 5

    Note: ki Dan bar ruwa kadan aciki kafin ki sauke yafi Dadi akan abar ruwan ya tsane Baki daya kaman shinkafa🤗🍽️

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Mrs IBY Favorite
Mrs IBY Favorite @cook_19496660
rannar
Kaduna

sharhai

Similar Recipes