ALALA (Nigerian moi-moi)

Firdausy Salees
Firdausy Salees @cook_12401542
Kano

Alalah...😉🤗yesss alala tamu din nan ta gargajiya 💃💃
Sae dae tasha wanka da zamani (next level)
Sabinta salon girkunanmu na gargajiya na kara fito mana da martabar tushenmu...♥️💃
Kuma zae bawa iyali marmarin cin abincin 💯

ALALA (Nigerian moi-moi)

Alalah...😉🤗yesss alala tamu din nan ta gargajiya 💃💃
Sae dae tasha wanka da zamani (next level)
Sabinta salon girkunanmu na gargajiya na kara fito mana da martabar tushenmu...♥️💃
Kuma zae bawa iyali marmarin cin abincin 💯

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

45mins
Mutane 5 yawan abinchi
  1. 2 cupsfarin wake
  2. 2kwae (eggs)
  3. Tattasae
  4. Attaruhu
  5. Albasa
  6. Tafarnuwa
  7. 1/2 cupmankuli (Veg oil)
  8. 1/2 cupmanja (palm oil)
  9. 1/2 tspgishiri (salt)
  10. 3sinadarin dandano(seasoning)
  11. 1/2 tspcurry
  12. 1/4 tspthyme
  13. Silicon moulds

Umarnin dafa abinci

45mins
  1. 1

    Ki jika wajenki ki gyara tass,ki fidda dusar kamar hka....

  2. 2

    Saeki saka attaruhu,albasa,tafarnuwa ki markada a blender/Ko ki kae a nika miki,nikan yayi laushi sosae kamar na kosae....

  3. 3

    Saeki juye markadadden waken acikin bowl mae dan girma kamar hka...

  4. 4

    Kisa gishiri,mankuli da manja...

  5. 5

    Kisa sinadarin dandano na ONGA da curry...

  6. 6

    Kisa thyme kadan hka da kwae guda 1 Ko 2,kisa sinadarin dandano guda 3 Ki juya kullin sosae yadda komae zae hade...

  7. 7

    Ki shafawa slicon moulds dinki manja/Ko gwangwani...

  8. 8

    Nan ga kullinmu da muka juya,muka buga sosae.saeki dinga diban ludayi daya kina zubawa aciki kamar hka...

  9. 9

    Ki shafawa (Slicon waffle maker) dinki manja Ki zuba kullin a gida biyu kawae,sannan ki rufo daya barin kamar hka....kisa ludayin juya waena gurin dauka ko ki fara saka maker din a steamer sannan kisa kullin.

  10. 10

    Kisa a steamer kiyi steaming dinshi na tsahon minti 15mins/20mins,yadda zaki gane y dahu idan kika taba saman zakijishi da tauri.

  11. 11

    Alhamdulillah alala y sauka saeki saka manja da yaji aci dadi lfy😉🙌

  12. 12
  13. 13

    Ga yadda cikin alalan mu yayi 🥰♥️💯

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Firdausy Salees
Firdausy Salees @cook_12401542
rannar
Kano

sharhai (11)

Ayshat Adamawa(U. Maduwa)
Ayshat Adamawa(U. Maduwa) @Ayshat_Maduwa65
@cook_12401542 ya ilahi pls come back to cookpad, we’re badly missing u

Similar Recipes