Bow tie buns

TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA) @cook_15480513
Port Harcourt

Nasamu wannan recipe wurin firdausy salis naji dadi sosai nida iyalaina kuma gashi da dadi ga laushi zaka iyayinsa ma bakima

Bow tie buns

Nasamu wannan recipe wurin firdausy salis naji dadi sosai nida iyalaina kuma gashi da dadi ga laushi zaka iyayinsa ma bakima

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

a/-2/5&6 yawan
  1. Fulawa kofi uku
  2. Yeast babban chokali daya
  3. Kawai biyu
  4. Madarar gari rabin kofi
  5. Bakin powder rabin chokalin shayi
  6. Gishiri dan kadan
  7. Sugar chokali uku
  8. Man gyada chokali uku
  9. Butter chokali biyu
  10. Vanilla flavor chokali daya
  11. Kwai daya don shafawa akai
  12. Da ridi don watsawa akai
  13. Hadin ciki nayi amfani da nikekken nama kamar hadin meat pie

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Dafarko zaki tankade fulawa kizuba a bowl sannan kizuba yeast da bakin powder da gishiri

  2. 2

    Sannan kizuba sugar da madara ki jujjuya komai yahade wuri daya

  3. 3

    Sannan kizuba kwai da flavor

  4. 4

    Sai kuma kizuba mai da ruwa sannan ki kwabashi

  5. 5

    Bayan kinkwaba sai kizuba butter akai kisake kwabawa sosai har nasawon minti biyar zuwa shida sannan ki ajiyeta tatashi. Bayan yatashi sai kuma kisake kwabawa sannan ki rabata gida uku ko hudu sai kidau daya kimurzata da fadi sosai sannan kisamo wani abu circle kicire shape din kamar haka

  6. 6

    Sannan sai kidauko hadin nikakken namanki kizuba akai sannan kirufeta ki daddana bakin yanda bazai budeba sannan kidauko wuka kiyankata kamar yanda nayi haka

  7. 7

    Sannan kidauko dayan gefen kidaura akai kamar yanda kikaga nayi sannan kisake daura dayanma akai sai kuma kidauko na sakiyan kidaura akai shima

  8. 8

    Sai kishafa butter a kwanon gasawarki sannan kijerasu akai sai kifasa kwai kikada sannan kishashshafa akai saikuma ki yaryada ridi akai sannan ki gasa

  9. 9

    Gashinan bayan nagasa aci dadi lfy

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
TEEGANA'S KITCHEN (FATIMABABAGANA)
rannar
Port Harcourt
Gskiya arayuwata inason girki sosai shiyasa kullum ina kicin wurin tsara abinci kalakala
Kara karantawa

Similar Recipes