Tura

Kayan aiki

  1. 3 cupsFlour
  2. 1/2 tspB.powder
  3. 1/2 cupButter
  4. Oil 3 tbp
  5. Attaruhu, albasa, tafarnuwa, citta
  6. 2Kwai
  7. Maggi,gishiri, sugar kadan, curry,
  8. Kifi
  9. Ganyen albasa
  10. Koren tattasai

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Zaki tankade flour kixuba a roba sai kisa baking powder gishiri da sugar kijujjuya sannan kisa butter ki mursika sosai sannan kisa kwai da ruwa sai kwabawa. Zakiyi kwabin kamar na meatpie ko doughnut. Bayan kinkwaba sai kirufe ki ajiye a gefe

  2. 2

    Sai kiwanke kifinki sannan kitafasa sai ki bari yahuce sannan kigyara kicire kayan duka sannan ki mursika tazama kanana sai ki ajiye agefe

  3. 3

    Sai kidaura pan a wuta sannan kisa mai chikali uku zuwa hudu sannan kizuba albasan da kika yanka kidan jujjuya sai ki jajjaga tafarnuwa da citta kizuba akai kijujjuya kibarta nadan lkci sannan kizuba jajjagen attarugu

  4. 4

    Bayan kinzuba attarugu kijujjuya sai kidauko kifin kixuba akai kisake jujjuyawa sai kisa maggi da sauran sinadaran kisake jujjuyawa sai kizuba lawashi kijujjuya sannan kisa koren tattase kijujjuya sai kibari yadahu sai kisauke ki ajiye agefe

  5. 5

    Sai kidauko dough naki kisake kwabawa sannan kiraba gida biyar sai kidau daya kimurza tayi fadi sai kidau wuka kirabashi biyu sannan kidauko hadin kifin kixuba a dayan gefen

  6. 6

    Sannan kinannade sai kidau wuka kiyankata sannan kishafa buttar a baking pan dinki sai ki jejjera akai

  7. 7

    Sai kidau chokali mai yatsu ki bubbula saman sannan kifasa kwai daya sai ki kada kishashshafa akai sannan kigasa

  8. 8

    Aci dadi lpy😋😋

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Sam's Kitchen
Sam's Kitchen @Sams_Kitchen
rannar
Yobe State
Cooking is my favorite
Kara karantawa

sharhai

Similar Recipes