Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. 10Kofi na flour
  2. 10 TBSmai
  3. 1ts na gishiri
  4. 2 TBSsukari
  5. 1albasa
  6. 3koren tattasai
  7. 21/2Kofi na ruwan dumi

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    Za'a tankade flour a roba me kyau a ajiye gefe, sai a wanke albasa da koren tattasai a gurzasu.

  2. 2

    Sai a zuba mai a cikin flour din a mutstsuka, sannan a zuba gishiri, sukari, koren tattasai da albasa suma a mutstsuka su a cikin flour din sannan a zuba ruwan dumi akwa6a. Sai a mulmulashi. A rufe a barshi zuwa wani lokaci

  3. 3

    Sai a dinga fadadashi sai a shafa mai a nadeshi kamar tabarma, a duquleshi kamar alkali a rufe shi nadan lokaci

  4. 4

    Sai a sake fadadashi idan yayi fale fale sai asa kwanon gashi a wuta asa chapati din anasa juyawa ana sa mai.

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Hauwa Dakata
Hauwa Dakata @hauwa1993
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes