Shinkafa da Miya

Jamila Ibrahim Tunau
Jamila Ibrahim Tunau @Jamitunau
Sokoto State

Wannan shinkafa da miya #gargajiya ce zalla bata buqatar kayan zamani

Shinkafa da Miya

Wannan shinkafa da miya #gargajiya ce zalla bata buqatar kayan zamani

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

1mintuna
2 yawan abinchi
  1. 2Shinkafa kofi
  2. Gishiri
  3. Miya
  4. Tumatur
  5. Tarugu
  6. Tattasai
  7. Albasa
  8. Tafarnuwa
  9. Nama
  10. Maggi
  11. Gishiri
  12. Mai

Umarnin dafa abinci

1mintuna
  1. 1

    Zaki aza ruwan zafi ki tabbata sun tafasa se ki debo shinkafa ki zuba ma shinkafar gishiri se ki wanke wannan shi zesa ko tayi ruwa bazata chabe ba kizuba idan ta tafasa kinji tafara kamshi se ki sauke ki tsane ruwan ga rariya sannan ki wanke se ki mayar a tukunya ki qara ruwa kadan sannan ki rage wuta ki rufe ki barta ta ta dahu shi ke nan ki sauke

  2. 2

    Zaki nika tumatur tarugu tattasai albasa da tafarnuwa se ki zuba mai a tukunya tare ki barsu suyi ta tafasa

  3. 3

    Se ki sama namanki maggi albasa da gishiri da daddawa ki tafasa idan namanki ya tafasa se ki hada da nikar ki ki rufe ki barta ta dahu sosai idan tumatur dinki nada tsami kisa kanwa kadan ko baking powder

  4. 4

    Da zarar miyar ki tayi zakiga mai ya taso se hadawa da shikafa wurin ci

Gyara girkin
See report
Tura
Cook Today
Jamila Ibrahim Tunau
rannar
Sokoto State
The kitchen is my comfort zone.
Kara karantawa

Similar Recipes