Tuwon shinkafa miyar alayyahu

Fateen
Fateen @Fteenabkr277
Tura

Kayan aiki

1:30mintuna
5 yawan abinchi
  1. 3Shinkafa kofi
  2. 2Fulawa Kofi
  3. Ruwa Iya yadda zai dafa miki
  4. Miyar taushe
  5. 30Alaiyahu na
  6. 40Tumatir na
  7. Tumatir na Leda rabi
  8. Attariku yadda kike so
  9. Man gyada
  10. Kayan kamshi
  11. Kayan dandano
  12. Kabewa na 20 ma ya isheki
  13. Nama yadda Allah ya hore miki
  14. Gyadar miya ishasshe

Umarnin dafa abinci

1:30mintuna
  1. 1

    Da farko bayan kin wanke tukunyarki sai ki daura kan wuta tare da ruwa.

  2. 2

    Sai ki zuba shinkafarki ki rufe Ki rage wuta Dan ya dafu a hankali

  3. 3

    Idan ta dahu sosai sai ki tuka amma ruwa ruwa sai ki zuba fulawarki Dan ya kameshi sosai kuma yayi laushi.

  4. 4

    Ki wanke alaiyyahunki ki tsige ki yanka manya ko kanana duk yadda kike so, ki yanka kabewanki

  5. 5

    Ki wanke yanka albasarki,ki daka tafarnuwa tare da attarigunki

  6. 6

    Sai ki fara daura tukunyarki mai tsabta ki zuba mai tare da albasa

  7. 7

    Ki zuba su tafarnuwa warki,attarigu, kabewa da maggi da dai duk kayan kamshin da kike so

  8. 8

    Sai ki Dan saka ruwa ki rufe har sai komai ya narke

  9. 9

    Idan komai ya narke sai ki zuba soyayyen naman ki, tare da ruwan nama ki rufe sai yayi daidai yadda idan kika saka alayyahun ba zaiyi ruwa ba.

  10. 10

    Idan yayi daidai sai ki zuba alaiyahunki

  11. 11

    Sai ki zuba gyadar miyarki. Ki barshi yayi kamar minti 5 shikenan kin gama

  12. 12

    Yadda zakiyi adon,zaki samu kwanonki irin shape din da kike so sai ki shafe shi da mai,ki dubo tuwanki ki saka mi mulmula sai ki bude tsakiyar da ludayi

  13. 13

    Sai ki fito da shi idan har tuwonki ya tuku da kyau babu abinda zaiyi lafiya zai fito

  14. 14

    Sai na dauko Dan karamin cokalina na shafe da mai

  15. 15

    Haka zakiyi duk wani ado da kike so

  16. 16

    Sai na zuba miyata a ciki

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Fateen
Fateen @Fteenabkr277
rannar

Similar Recipes