Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. Biskin alkama
  2. Man gyada
  3. Kindirmo
  4. Sugar
  5. Tsamiya
  6. Kanwa

Cooking Instructions

  1. 1

    Kisamu alkama ki kai a surfa miki,bayan an sufar sai ki wanke ki shanya ta ta bushe daga nan sai ki kai inji a barza miki

  2. 2

    Bayan an barza miki ki dauki man gyadan ki kizuba(kisa mai gyadan da dan dama saboda alkakin yayi laushi) sai kiyi ta murzawa har sai ya hadu daga nan ki xuba kindirmo da dan ruwa sai ki kwaba amma ki kwaba da tauri sosai.shi alkaki anfi son a kwaba shi ya kwana soboda ya jika sosai.

  3. 3

    I dan safiya tayi sai ki jika kanwa.ki samu turminki da kika wanke sannan sai ki dauki kwabinki ki sa a turmi sai ki yayyafa jikakken kanwa ki da dan ruwa sai ki fara kirbawa.ki kirba sosai har sai yayi danko sasai,har sai ki tsinka ki gwada nadewa ki kaga ya nadu ba tare da ya karye ba.Idan ya karye sai ki mayar cikin turmi ki kara yayyafa ruwa ki cigaba da kirbawa har sai yayi laushi da danko

  4. 4

    Ki jika tsamiya.ki samu sugar ki sa a wuta har sai ya narke,Idan sugar ya narke sai ki zuba ruwa jikakken tsamiyan,da dan ruwa yadan saboda ya rage kauri amma kar yayi ruwa sosai sai ki sauke ki aje a gefen wuta

  5. 5

    Ki daura mai gyadan a wuta,Idan mai yayi zafi sai ki dauko alkakin ki da kika nannade a shape inda kike so sai ki fara suya.ki soya kar sai yayi golden Brown kina cirewa sai sa a ruwan sugar ki jujjuya sosai sai ki barshi a cikin ruwan sugar yayi kaman minti 5 daga nan zaki iya cirewa, alkaki is ready

Edit recipe
See report
Share
Cook Today
Teemerh's Cuisine
Teemerh's Cuisine @teemerh_cuisine
on
Biu,Borno State

Comments (3)

Ummu haifa
Ummu haifa @08139604460F
Ba'a saka yeast ko baking powder

Similar Recipes