Wainar Rogo na (D'anyen Rogo)

Rahma kabir
Rahma kabir @rahmakabir
Kaduna

#Kadunastate. Wainar rogo ko (k'osan rogo) na D'anyen rogo yafi na garin kwaki dad'i domin shi yana da dank'o da taushi. Aci da yaji ko miyar Albasa da tarugu. Yummyyyy.

Wainar Rogo na (D'anyen Rogo)

#Kadunastate. Wainar rogo ko (k'osan rogo) na D'anyen rogo yafi na garin kwaki dad'i domin shi yana da dank'o da taushi. Aci da yaji ko miyar Albasa da tarugu. Yummyyyy.

Edit recipe
See report
Share
Share

Ingredients

  1. D'anyen Rogo
  2. Tarugu
  3. Jan tattasai
  4. Albasa
  5. Maggi
  6. Gishiri
  7. Spices
  8. Mai
  9. Yaji ko
  10. Miyar Albasa da Tarugu

Cooking Instructions

  1. 1

    Zaki b'are rogo ki jikashi a ruwa, ki wanke sai ki yanka shi k'anana ki jajjaga a turmi ki kwashe sai ki kai maikad'e.

  2. 2

    In an kawo markad'en ki sanya a abin tace koko ki matse ruwan in ya fita ki zubar, saiki juye rogon a roba mai kyau.

  3. 3

    Kin jajjgara tattasai, tarugu da albasa saiki zuba a cikin rogon, ki sanya maggi gishiri da spices ki juya shi da kyau.

  4. 4

    Sai ki rik'a d'iba kina tab'ashi da hannunki kina jerawa a tire harki gama duka saiki fara suya.

  5. 5

    Kisa Mangyad'a a wuta mai yawa ki yanka albasa ki jefa a ciki, in albasan ta soyu saiki fara suyar wainar rogonki kamar haka

  6. 6

    Da ya soyu yayi brown color saiki kwashe ki sanya a matsami mai ya tsane, sai ki zuba a mazubi, sai ci da yaji ko miyar albasa da tarugu. Akwai dad'i sosai.

Edit recipe
See report
Share

Cooksnaps

Did you make this recipe? Share a picture of your creation!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Rahma kabir
Rahma kabir @rahmakabir
on
Kaduna
I love cooking.
Read more

Comments

Similar Recipes