Meat pie

Hauwa Dakata
Hauwa Dakata @hauwa1993
Kano

Wannan girkin nasameshine a gurin Aisha Adamawa daya daga cikin masu kulawa da Cookpad ta bangaren Arewacin Nigeria. Ni da yarana muna godiya Allah ya qara basira amin.

Meat pie

Masu dafa abinci 2 suna shirin yin wannan

Wannan girkin nasameshine a gurin Aisha Adamawa daya daga cikin masu kulawa da Cookpad ta bangaren Arewacin Nigeria. Ni da yarana muna godiya Allah ya qara basira amin.

Gyara girkin
See report
Tura
Tura

Kayan aiki

  1. Nama
  2. Dankalin turawa
  3. Albasa
  4. Karas
  5. Attaruhu
  6. Kayan kamshi
  7. Kayan dandano
  8. Sai abubuwa bukata na dough
  9. 3Fulawa kofi
  10. 125 grButter
  11. 3Kwai
  12. Gishiri
  13. Hodar gashi 1 teaspoon

Umarnin dafa abinci

  1. 1

    A fere dankali a yankashi a tafasashi da dan gishiri a ajiye a gefe. A fere karas a yankashi a tafasa da gishiri shima a ajiye a gefe. A yanka albasa sai a sata a tukunya a hada da nama da kayan dandano da attaruhu a basu tsoro da dan mai sai a zuba ruwa kadan a juye kara da dan kalin da aka tafasa a barsu su dan dahu tare idan ya qafe sai a sauke.

  2. 2

    Za'a tankade fulawa tare da hodar gashi, sai a saka gishi da butter a cakudasu tare idan butter din ya hade da folawa sai a fasa kwai guda biyu a kadashi a zuba akwa6in fulawa acigaba da muzawa sai asa ruwa kadan dan folawar ta hade jikinta. A yankata a murza a adinga zuba naman ana like bakin fulawar da aka murza.

  3. 3

    Daya kwain sai a fasa shi a wani abu a kadashi ayi amfani da brush ashafa a bayan meat pie din, za'a yi amfani da farantin gashi amma sai an shafeshi da butter sai a jere meat pie din a gasashi.

Gyara girkin
See report
Tura

Cooksnaps

Shin kunyi wannan girkin? Raba hoton naku girkin!

Grey hand-drawn cartoon of a camera and a frying pan with stars rising from the pan
Cook Today
Hauwa Dakata
Hauwa Dakata @hauwa1993
rannar
Kano

sharhai

Similar Recipes